<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Ba da Labarin Mutuwar Yesu LW271</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ba da labarin mutuwar Yesu,
 Jini ya bayar domin cetonmu,
 Amma ya tashi, ya ci nasara,
 Ceto za a samu wurinsa kaɗai.

[V2]
 KORUS
 Ba su labari, ba su labari,
 Yawancinsu ba su ji ba.
 Masu zunubi su tuba su bi shi,
 Yesu Mai Cetonsu ne.

[V3]
 2) Ba da labari ga mazaje duk,
 Ba za su tsira ba, sai dai sun ji.
 Ba da labari a wurin mata,
 Don su ma su tuba su ba da gaskiya.
 Korus

[V4]
 3) Ba da labari don yara su ji,
 Su ƙanƙanana su gane su bi.
 Ko masu yawa, ko ɗaya kaɗai,
 Mu ba su labari da ƙwazo sosai.
 Korus

[V5]
 4) Ba da labari ga duk mutane,
 Ko sun ji daɗi, ko wasu sun ƙi.
 Yi ta addu'a da bangaskiya,
 Maganarsa tana da iko sosai.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>271</hymn_number>
</song>